Sports
Chelsea za ta fafata da Real Madrid
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Kungiyar Real Madrid wadda ta zama gwarzuwa a gasar zakarun Turai za ta kara da Chelsea da ta lashe gasar a bara.
Manchester city za ta kara da Atletico Madrid, yayin da Liverpool za ta barje gumi da Benfica sai kuma wasan Bayern munich da Villarreal.
Za a buka wasannin a ranar 5 da 6 ga watan Afrilu sai kuma 12 da 13 ga Afrilun wannan shekarar.
Za kuma a fafata a wasan kusa da na karshe a ranakun 26-27 sannan a buga na biyu a ranar 3-4 ga watan Mayu mai zuwa.
Za a buga wasan karshe na gasar a filin wasa na Stade de France da ke Faransa a ranar Asabar 28 ga watan Mayu, bayan dauke shi da ka yi daga St Petersburg bayan fara mamayar Rasha a Ukraine
Wasa kusa da daf da na karshe
Chelsea da Real Madrid
Manchester City da Atletico Madrid
Villarreal da Bayern Munich
Benfica da Liverpool
Wasan kusa da na karshe
Manchester City v Atletico Madrid v Chelsea or Real Madrid
Benfica da Liverpool v Villarreal or Bayern Munich
