Connect with us

News

Rabin Al’ummar Duniya Sun Fuskanci Matsanancin Zafi Saboda Sauyin Yanayi — RAHOTO 

Published

on

images
Advertisements
ads

Wani sabon rahoto da ƙwararrun masana kan sauyin yanayi suka fitar ya bayyana cewa a cikin shekara guda da ta gabata, rabin al’ummar duniya – wato kusan mutane biliyan huɗu – sun fuskanci matsanancin zafi fiye da kima.

Rahoton ya bayyana cewa daga ranar 1 ga watan Mayu, 2024 zuwa 1 ga watan Mayu, 2025, mutane a sassa daban-daban na duniya sun shiga mawuyacin hali sakamakon dumamar yanayi da aka danganta da ayyukan ɗan Adam, musamman gurɓatar da ake yi ta hanyar amfani da makamashi masu fitar da hayaƙi.

KULA DA MARAYU: Hanya Ce Ta Samun Rahamar Ubangiji – Malam Ja’afar

Masana sun ce irin wannan matsanancin zafi bai taɓa faruwa ba a baya, inda suka ce ya ninka kashi 90 cikin 100 na irin yanayin zafin da duniya ta fuskanta tsakanin shekarar 1991 zuwa 2020.

Rahoton ya ce dumamar yanayin ta haddasa mutuwar mutane da dama, ta haifar da yaduwar cututtuka, sannan ta lalata gonaki da amfanin gona da yawa da gobara ta ƙone.

A watan Maris, an fuskanci matsanancin zafi a yankin Tsakiyar Asiya, sai kuma tekun Maditaraniya a watan Yuli, da kuma Sudan ta Kudu a watan Fabrairu.

A Morocco, akalla mutane 21 ne suka rasa rayukansu a bara saboda tsananin zafi da aka fuskanta a watan Yuli – abin da masana suka ce ba zai faru ba da sauƙi, sai dai idan akwai tsananin dumamar yanayi da ayyukan ɗan Adam ke haifarwa.

Advertisement

Rahoton ya sake jaddada buƙatar gaggauta ɗaukar matakai na rage dumamar yanayi, musamman dakatar da amfani da makamashin da ke fitar da hayaƙi mai gurbata iska, tare da rungumar hanyoyin samar da makamashi masu tsafta.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending