News
Jihohin Da Za A Iya Fuskantar Ambaliya A Najeriya Cikin Watan Yuni — NiMet
Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta yi hasashen yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu sassan Najeriya, musamman jihohin da ke yankin arewa ta tsakiya, a cikin watan Yuni na shekarar 2025.
A cikin wani rahoto na musamman da ta fitar a ranar Lahadi, hukumar ta bayyana cewa akwai alamun saukar ruwan sama mai yawa a cikin ɗan gajeren lokaci a wasu jihohin, abin da ka iya janyo ambaliya, musamman a wuraren da ke cikin haɗari.
Rikici Kan Tambarin Shayi Na Barazana Ga Aikin Sama Da Matasa 500 A Kano
“Jihohin da aka fi hasashen samun marka-markan ruwan sun haɗa da Nasarawa, Filato, Bauchi, Jigawa, Kaduna, Kano, Kebbi da Babban Birnin Tarayya (FCT),” in ji NiMet.
Hasashen ya zo ne a daidai lokacin da ƙasar ke ci gaba da jimamin mummunar ambaliyar da ta afku a jihar Neja, inda rahotanni ke nuna cewa mutane sama da 500 ne suka rasa rayukansu.
NiMet ta bukaci jama’a da su kasance a shiri, tare da bin shawarwari da bayanan da hukumar ke fitarwa a kai a kai domin kariya daga illar ambaliya. Hakanan ta shawarci hukumomin da ke kula da madatsun ruwa da su sanya ido tare da lura da yawan cikowar ruwa a matattarar ruwa.
Rahoton ya ƙara da cewa za a samu ruwan sama mai ƙarfi da iska a wasu sassan jihohin kudu da arewa ta tsakiya, amma hakan ba zai kai matakin da aka saba samu a wasu jihohin ba.
“Jihohin Kwara, Kogi, Neja, Nasarawa, Benue, Taraba, Adamawa, Kaduna, Kano, Katsina, Sokoto, Edo, Delta da Abuja ba za su samu ruwan sama mai yawa kamar yadda aka saba a wasu lokuta ba,” in ji NiMet.
Daga ƙarshe, hukumar ta shawarci manoma da su yi amfani da ilimin zamani da ƙwarewa wajen gudanar da harkokin noma, domin kauce wa asara sakamakon sauyin yanayi da ake fuskanta.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
