Connect with us

News

NDLEA Ta Kama Mutane 36 Kan Laifin Safarar Kwayoyi A Kano

Published

on

Wasu Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Babban Jami’in Hukumar NDLEA

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), reshen jihar Kano, ta cafke mutum 36 bisa zargin safarar nau’o’in miyagun ƙwayoyi daban-daban a wani gagarumin samame da ta gudanar a sassan jihar.

Mai magana da yawun hukumar, Malam Sadiq Muhammad-Maigatari, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa samamen ya gudana ne a ranakun 30 da 31 ga watan Mayu.

‎Rikici Kan Tambarin Shayi Na Barazana Ga Aikin Sama Da Matasa 500 A Kano

Ya ce daga cikin wuraren da jami’an suka kai samame akwai Maƙabartar Ɗan’agundi, kasuwar Kwari, Ƙofar Na’isa da kuma Kano Line — dukkansu kafin lokacin bukukuwan Sallah.

 

A cewarsa, an kama waɗanda ake zargin ne tare da buhunan tabar wiwi, sukurkudan sukudaye, diazepam, sholisho da sauran sinadarai da doka ta haramta.

 

Advertisement

Kwamandan hukumar a jihar Kano, Kwamanda Abubakar Idris-Ahmad, ya jinjinawa jami’an da suka taka muhimmiyar rawa wajen nasarar samamen, tare da bukatar al’umma su yi bikin Sallah cikin kwanciyar hankali da natsuwa ba tare da amfani da ƙwayoyi ba.

 

Ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa bayar da rahoto kan duk wani motsi da ake zargin yana da nasaba da fataucin miyagun ƙwayoyi, domin tabbatar da tsaron lafiyar al’umma da zaman lafiya a jihar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending