News
RANAR MUHALLI TA DUNIYA: Masana Sun Yi Kira Da A Dauki Mataki Kan Yawaitar Dattin Robobi A Kano
Masana da ƙungiyoyi masu zaman kansu sun bayyana damuwa kan yadda ake kara yawaitar datti, musamman na robobi a jihar Kano, yayin bikin Ranar Muhalli ta Duniya da ake gudanarwa a duk shekara a ranar 5 ga Yuni.
Taken bikin na bana shi ne “Dakile Gurguntar Muhalli da Dattin Roba”, kuma an gudanar da taron ne a Tahir Guest Palace, Kano, karkashin hadin gwiwar Ma’aikatar Muhalli ta Kano da UK International Development (ta shirin SFC da PACE).
Bukola Saraki Ya Aika Tallafi Zuwa Ga Wadanda Ambaliya Ta Shafa A Mokwa
A cewar Dr. Bello Abba Yakasai, Najeriya na fitar da tan miliyan huɗu na datin roba a shekara, kuma jihar Kano na da tan dubu 30 daga cikinsu.
“Wannan abu ne mai matuƙar hadari, domin dattin roba na shiga ruwa da abinci da kuma jinin dan adam,” in ji wani masani, Dr. Umar Sale Anka.
Masana sun bayyana cewa akwai buƙatar a haramta amfani da robobi da ake amfani da su sau ɗaya, sannan a tilasta wa kamfanoni su rika kula da sharar da suke fitarwa.
Ambasada Dr. Sani Usaini ya ce sauyin yanayi da gurbacewar muhalli na kara jefa rayuwar talakawa cikin hadari, inda ya bayyana cewa cututtuka da matsin rayuwa na kara yawa sakamakon haka.
Gudunmawar UNICEF da Jama’a
Rahma Muhammad Farah daga UNICEF ya ce sun shuka fiye da itatuwa 100,000 a makarantu domin rage tasirin sauyin yanayi da kare lafiyar yara.
“Yara su ne suka fi shan wahala idan sauyin yanayi ya yi tsanani,” in ji shi.
Shugaban ƙungiyar PACE, Auwal Hamza, ya ce sai kowa ya bada tashi gudunmawa wajen rage sharar da muke fitarwa, musamman ta hanyar sake amfani da ita.
“Ba aikin gwamnati kaɗai ba ne, kowa na da rawar takawa,” in ji shi.
Taron ya samu halartar masana daga jami’o’i da hukumomi, inda aka tattauna hanyoyin magance matsalar sharar roba, da kuma ƙarfafa dokokin kare muhalli.
An kuma gudanar da muhawara tsakanin daliban makarantu, inda suka nuna fasaha da basira kan yadda za a kare muhalli.
A ƙarshe, an bai wa ƙungiyoyin da suka bada gudummawa kyaututtuka, ciki har da UNICEF, PACE da SFC.
