News
Za Mu Maka Sarki Sanusi II A Kotu Kan Rakiyar Gungun Matasa Dauke da Makamai – Cewar Lauya Salisu Umar
Wani lauya a jihar Kano, Barista Salisu Salisu Umar, ya bayyana aniyar su ta gurfanar da Mai Martaba Sarkin Khalifa Muhammadu Sanusi II, a gaban kotu, dangane da yadda wasu gungun matasa da ake kyautata zaton ‘yan daba ne suka rakashi yayin Hawan Fanisau da ya gudanar, dauke da makamai a hannayensu.
Barista Salisu ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai a yau, inda ya bayyana damuwar sa kan yadda al’amura ke gudana a jihar Kano, musamman yadda wasu matasa ke amfani da irin waɗannan taruka wajen nuna karfi da tayar da hankali.
Ana Zargin Wata Uwa Da Ajalin ’Yarta Akan Naira 100 A Zariya
“Ba wai muna cewa Sarki ne ke daukar nauyin ‘yan daba ba, amma yadda aka ga wasu gungun matasa dauke da makamai suna rakiyar hawan nasa, abin damuwa ne matuka. Wannan lamari na iya zama barazana ga zaman lafiya da doka da oda,” in ji Barista Salisu.
Wannan abu ne da ya kamata kuwa yayi Allah wadai da shi domin yana iya janyo hargitsi, tashin hankali, da kuma raini ga bangaren shari’a.
Wannan lamari na kara nuna cewa akwai wasu gungun Shugabannin masu hannu a harkokin tada zaune tsaye a jihar Kano. Tunda nake, ban taba ganin gungun matasa dauke da makamai a lokacin Hawan Sallah kamar haka ba.”
Duk Da Haramtawar ‘Yan Sanda, Sarki Sanusi II Ya Gudanar Da Hawan Fanisau
Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ci gaba da gudanar da al’adar Hawan Fanisau, duk da dokar hana hakan da rundunar ‘yan sanda ta bayar. A bana, an gudanar da hawan ne ta hanyar amfani da jerin gwanon motocin masarauta maimakon dawaki, kamar yadda aka saba a da.
Rahotanni na nuni da cewa titunan Kano sun cika da jama’a da suka fito domin shaida wucewar Sarki, lamarin da ya jawo fargaba a tsakanin wasu mazauna birnin, ganin yadda wasu matasa ke bin jerin motocin da makamai a hannunsu
Tun cikin shekarar 2024, rundunar ‘yan sandan Kano ke hana gudanar da Hawan Sallah da dawaki saboda barazanar tsaro. Wannan umarni ya shafi dukkan sarakuna da masarautu, amma a bana, an ga Sarki Sanusi II ya gudanar da hawan nasa cikin motocin masarauta.
Masu fashin baki na cewa wannan lamari na kara dagula lamarin masarautar Kano, musamman a daidai lokacin da ake fama da rikicin bangarori biyu masu goyon bayan sabuwar doka da na tsohuwar masarauta.
