News
APC NA FARFAGANDA, GWAMNATI NA AIKI: Yunkuri Ne Na Kawar Da Hankalin Jama’a Daga Ayyukan Gwamnatin —Eye On Kano
Wani yunkuri da wata ƙungiya a jam’iyyar APC mai suna APC Patriotic Volunteers ke yi na caccakar gwamnatin Kano da zargin karɓar bashi daga ƙasashen waje har Dala Miliyan 6.6, ya gamu da raddi mai zafi daga ƙungiyar Eye on Kano Initiative, wacce ta bayyana wannan mataki a matsayin ƙarairayi da ƙoƙarin karkatar da hankalin al’umma daga abinda ke faruwa a zahiri cikin jihar.
ZARGIN RASHIN AIKI: Yunkuri Ne Na Kawar Da Hankalin Jama’a Daga Ayyukan Gwamnatin Kano — Eye on Kano
Ƙungiyar ta ce, tun bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya hau mulki ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, gwamnatin Kano ta rungumi gaskiya da aiki da hannu biyu, tare da fuskantar kalubale da gyara baraguzan da gwamnatin da ta gabata ta bari.
Bashi: Sun Faɗi, Amma Ba Su Bayyana Ba
A wani taron manema labarai da shugaban ƙungiyar APC Patriotic Volunteers, Alhaji Usman Alhaji ya kira a Kano, ya zargi gwamnatin NNPP da cewa ta karɓi bashi daga ƙasashen waje ba tare da bayani ba. Amma a martanin da Eye on Kano ta fitar, ta ce wannan zargi ba ya da makama, domin kuwa babu wani sabbin bashi da aka ɗauka tun hawar gwamnatin yanzu – sai dai irin tarin bashin da gwamnatin baya ta bari.
> “Idan suna da hujja, su fito da takardun DMO, su bayyana yadda kuɗin suka fito, daga wane lokaci, da kuma yadda gwamnatin yanzu ta karɓa – kar su rufe gaskiya da inuwa.”
Kudaden Muhalli: An Watsar Da Su a Baya, Yanzu Ana Amfani da Su
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa kudaden muhalli na Naira biliyan 5.1 da gwamnatin tarayya ta fitar, an yi amfani da su wajen gyaran kwatance a Bulbulawa da Wailari, aikin magance ambaliya, da kuma gyaran hanyoyi a wasu unguwanni da suka daɗe cikin halin kunci.
> “Wanda suka jefa jihar cikin ɗumamar laka, yanzu su ke ƙoƙarin hana ta ficewa cikin ruwan sanyi,” in ji sanarwar.
“Yin Shiru Akan Ƙarya, Barazana Ne Ga Zaman Lafiya”
A cikin rahoton, Eye on Kano ta jaddada cewa gwamnatin NNPP ba za ta tsayawa kare kanta daga farfaganda ba, domin kuwa ayyuka na ƙasa sun isa su kare duk wani shugabanci nagari. Ta ce jam’iyyar da ta yi shiru lokacin da ma’aikata ke mutu ba tare da fansho ba, malamai suna gajiya da yunwa, da kuma ruwan sha ya zama kamar zinariya, yau ita ce ke magana.
> “An yi rikon sakainar kashi a baya, amma yanzu ana bin doka da oda. Jama’a sun farka.”
Masarautu, Kananan Hukumomi da Tsarin Mulki: Doka Ce Ke Magana
Dangane da matsalolin da suka shafi masarautu da kananan hukumomi, Eye on Kano ta ce gwamnatin yanzu ba ta da wani abu da take yi da gaban kanta. Komai a gaban kotu yake, kuma an bai wa doka dama ta yi aiki. Wannan kuwa shi ne ginshiƙin shugabanci nagari.
Gaskiyar Aiki Ta Fi Magana
Ƙungiyar ta bayyana wasu daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin NNPP ta aiwatar da su cikin shekara biyu:
Sayo pampuna 10 masu ƙarfi da haƙar rijiyoyi 6 na masana’antu don samar da ruwa.
Kashi 31% na kasafin kuɗi na 2025 an ware shi ga ilimi.
Gina da sabunta daruruwan azuzuwa a fadin jihar.
Farfado da tsarin IPP don samar da haske a wuraren zama.
Dawo da kadarorin gwamnati da aka sayar ba bisa ka’ida ba.
Kare martabar kafafen yaɗa labarai tare da hana yaɗa ƙarya da cin mutunci.
Aiwatar da doka kan biyan albashi da fansho.
A ƙarshe, Eye on Kano ta bayyana cewa gwamnatin da ke aiki ba ta buƙatar kare kanta da hayaniyar ƙarya. A cewarta, ayyukan da ake gani da ido, da yadda gwamnatin ke buɗe littattafai ga jama’a, sun isa shaidar cewa gwamnatin NNPP tana tafiya bisa gaskiya da amana.
> “Ba wai gwamnati ce ke neman wanke kanta ba – aiki ne ya riga ya yi magana. Wanda ba su da aikin faɗa, su ɗan tsaya a kalla su koyi gaskiya.”
