News
Jami’an Tsaro Sun Kama Masu Satar Waya A Kano, Sun Kwace Babura Guda Biyu
Rundunar Jami’an Tsaro ta Musamman da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa domin yaƙi da satar waya da fataucin miyagun ƙwayoyi, ta cafke matasa huɗu da ake zargi da aikata wannan laifi, tare da kwace babura masu ƙafafu uku guda biyu da ake amfani da su wajen aikata laifukan.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Musamman ta jihar Kano, Malam Muhammad Dahir Idris, ya fitar a ranar Talata.
Gwamnati Ta Ayyana Laraba A Matsayin Ranar Hutu Ga Ma’aikata Bisa Ziyarar Tinubu
Sanarwar ta bayyana cewa, an cafke mutanen ne da yammacin Litinin da misalin ƙarfe 8:00 na dare, a yankin Hadejia Road da Eastern Bypass, yayin wani atisaye na musamman da rundunar ta gudanar.
Shugaban Rundunar, Manjo Janar Gambo Ahmad Mai’adua (rtd), ya bayyana cewa waɗanda ake zargi sun saci waya daga hannun wani mai wucewa, kuma an cafke su yayin da suke ƙoƙarin tserewa da babura.
Ya ƙara da cewa an kwato babura guda biyu da ake zargin su ke amfani da su wajen aikata satar wayoyi.
A cewar sanarwar, a wani lamari makamancin haka da ya faru a Hadejia Road, rundunar ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da kai hari kan wani jami’in tsaro, wanda yanzu haka ke karɓar magani a asibiti.
Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Musamman na Jihar Kano, Air Vice Marshal Ibrahim Umaru (rtd), ya yaba da namijin kokarin rundunar, tare da jaddada cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da mara wa jami’an tsaro baya domin tabbatar da doka da oda a fadin jihar.
