News
Iran ta yi wa sansanonin sojojin Amurka da ke Qatar da Iraqi luguden makamai masu linzami
Iran ta harba makamai masu linzami kan sansanonin Amurka da ke Qatar da Iraki, kamar yadda gidan talabijin na Iran ya ruwaito, a daidai lokacin da wasu manyan bama-bamai suka tashi a Doha, babban birnin Qatar.
PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa Iran ta sha alwashin mayar da martani bayan da Amurka ta kai hari kan wasu manyan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku a ranar Lahadi.
Koriya Ta Arewa Za Ta Taimaka Wa Iran Wajen Gyara Tashoshin Nukiliyarta
Ba a dai san illar hare-haren na Iran ba har zuwa lokacin da ake wannan rahoto amma BBC ta ruwaito cewa an ji karar fashewar wasu abubuwa a Qatar inda Amurka ke da sansaninta na Al Udeid.
Tun da farko dai Amurka da Birtaniya sun gargadi ‘yan kasarsu da ke Qatar da su kiyaye yadda za zirgazirgarsu inda Amurka ta ce tana da rahotannin cewa Iran za ta kai hari kan muradunta a Qatar.
Qatar ta kuma rufe sararin samaniyarta na wani dan lokaci ga dukkan jiragen.
