Connect with us

News

Prof. Gwarzo Ya Bai Wa Cibiyar Koyar Da Harshen Faransanci Ta  Alliance Francaise Ofishi A Kano

Published

on

IMG 20250627 WA0139 735x400

Shugaban rukunin Jami’o’in MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bai wa cibiyar koyar da harshen Faransanci ta Alliance Francaise da ke Kano gini mai hawa biyu domin zama ofishinta na dindindin.

Prof. Gwarzo ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa ginin da ke kan titin Filin Jirgin Sama, kusa da unguwar Ahmadiyya a Kano, yanzu ya koma mallakin Alliance Francaise.

“Mun cimma matsaya da Gwamna Fubara, mun yanke shawarar aiki tare” —Wike

Ya ce wannan mataki na daga cikin kokarinsa na tallafa wa ci gaban koyon harshen Faransanci a Kano, musamman ganin irin rawar da cibiyar ke takawa wajen bunkasa ilimin yare da al’adu tsakanin Najeriya da Faransa.

“Alliance Francaise ta shafe fiye da shekaru 30 tana aiki a Kano ba tare da mallakar ofishi na dindindin ba. Wannan ne ya sa na yanke shawarar bayar da wannan gini domin taimakawa su samu wuri na dindindin,” inji shi.

Prof. Gwarzo ya ce an tanadi dukkan kayan more rayuwa da ake bukata a cikin ginin, ciki har da kayan daki da kuma tsarin samar da wutar lantarki ta hasken rana domin tabbatar da ingantaccen aiki.

Ya bayyana cewa wannan tallafi nasa wani mataki ne na yin koyi da babban dan kasuwa daga Legas, Mike Adenuga, wanda ya taba bayar da gini ga Alliance Francaise a Legas.

Advertisement

Farfesan ya ce yana da yakinin cewa wannan gudummawa za ta taimaka matuka wajen habaka koyar da harshen Faransanci a Kano da ma Najeriya baki daya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending