News
An Gurfanar da Matashi Bisa Zargin Yunkurin Kashe Kansa A Kan Allon Talla A Kano
Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta gurfanar da wani matashi mai shekaru 19, Ibrahim Abubakar, a gaban Kotun Majistire da ke unguwar Gyadi-Gyadi, bisa zargin yunkurin kashe kansa ta hanyar hawa saman wani dogon allon talla a gadar Ado Bayero da ke cikin birnin Kano.
Rahotanni sun nuna cewa, matashin wanda ya fito daga jihar Adamawa, ya hau kan allon tallar ne yana barazanar jefa kansa kasa, inda ya bayyana cewa sai dai idan ya ga wani shahararren ɗan TikTok, Abdul BK, kafin ya sauko daga saman allon.
Kwankwaso Na Fakewa da Talakawa Domin Cimma Burinsa, – Adnan Mukhtar
A cewar sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya wallafa a shafinsa na Facebook, an kama matashin ne a farkon makon nan, bayan da jami’an tsaro suka yi ta kokarin shawo kansa ya sauko daga saman allon.
SP Kiyawa ya bayyana cewa, an gurfanar da Ibrahim Abubakar a gaban Kotun Majistire mai lamba 5 da ke unguwar Gyadi-Gyadi, inda ake tuhumarsa da laifin yunkurin kashe kansa.
A cewar SP Kiyawa, wannan lamari ya tayar da hankalin al’ummar yankin tare da haddasa cunkoso da taruwar jama’a a wajen da abin ya faru.
Ya ce, irin wannan aiki na iya jefa mutane cikin tsoro da firgici, sannan kuma yana hana gudanar da harkokin yau da kullum a yankin.
Kotun ta dage sauraron karar zuwa wani lokaci domin ci gaba da bin diddigin shari’ar.
