Connect with us

Politics

Tsoffin Shugabannin PDP Sun Caccaki Gwamnatin Shugaba Tinubu

Published

on

1751398127754

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP sun gudanar da wani muhimmin taro a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja, domin nazarin halin da jam’iyyar ke ciki da kuma fitar da wata hanya gabanin zaɓen 2027. Taron ya gudana a ranar Talata 1 ga watan Yuli, 2025.

Cikin waɗanda suka halarta akwai tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark, tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido, Uche Secondus, Tambuwal, Liyel Imoke, Babangida Aliyu da Sam Egwu, tare da wasu manyan shugabannin PDP daga faɗin ƙasar nan. Sun tattauna kan gazawar jam’iyyar tun bayan faduwar zaɓe da kuma yadda gwamnatin APC ke amfani da hukumomi wajen murkushe adawa.

Advertisement

Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Na Best Choice Ya Rage Kaso 50 Na kuɗaɗen Ayyukansu Tare Da Buɗe Fayal Kyauta

Jiga-jigan PDP sun bayyana damuwa kan rashin daidaito da raunin shugabanci da suka ce ya rage wa jam’iyyar ƙarfi, tare da barazana ga dimokuraɗiyya da tattalin arzikin ƙasa. Sun ce Najeriya na bukatar sabuwar hanya domin farfado da martaba da ci gaban da ake fata.

Sai dai ba a bayyana cikakken mataki da aka cimma ba, amma majiyoyi sun ce ana duba yiwuwar kafa sabuwar haɗaka da za ta kalubalanci gwamnatin Tinubu a zaɓen 2027, ko kuma sabunta tsarin PDP daga ciki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending