News
’Yan Sanda Sun Kama Matasa 5 Da Ake Zargi Da Kwacen Waya A Adaidaita Sahu A Kano
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama matasa biyar da ake zargin suna kwace wa mutane wayoyi da sauran kayayyaki a cikin birnin Kano, ta hanyar amfani da babura kirar Adaidaita Sahu.
Bayanan da aka samu sun nuna cewa biyu daga cikin wadanda ake zargin an kama su ne a yankin Kofar Ruwa, bayan da jama’ar unguwar suka yi ram da su lokacin da suka yi ƙoƙarin kwace waya daga hannun wani matashi.
Ko Tinubu Ya Nada Ɗansa Seyi Tinubu Shugaban INEC, Sai APC Ta Fadi A 2027 – Dalung
Wani ganau ya ce, “Sun dade suna yi mana haka, amma yau an kamo su, muka tsare su har sai da ’yan sanda suka zo suka dauke su.”
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai jan hankalin jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu.
“An kama su. Amma don Allah a daina ɗaukar doka a hannu,” in ji SP Kiyawa a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
A wata sabuwar sanarwar SP Kiyawa, ya tabbatar da cewa karin mutum uku da ake zargin suna cikin wata tawaga ta masu kwace waya, suma an cafke su a yankin Kano Line, tare da baburinsu kirar Adaidaita Sahu da ake zargin suna amfani da shi wajen aikata laifuka.
Yanzu haka dukkan su biyar suna hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike a kansu kafin a gurfanar da su a gaban kotu.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
