News
Hisbah Ta Kama Mota Ɗauke Da Giya Ta Sama Da Naira Miliyan Hudu A Kano
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wata mota mai lamba MKA 919 YZ da ke ɗauke da katon-katon giya a karamar hukumar Dawakin Tofa, lamarin da hukumar ta ce ya faru ne yayin wani samame da ta gudanar bisa sahihan bayanai da ta samu.
A cewar hukumar, an ƙiyasta darajar giya ɗin da aka kama a kimanin naira miliyan hudu da dari hudu (₦4,400,000).
Mataimakin Babban Kwamandan hukumar, Dakta Mujahideen Abubakar, ya tabbatar da kamen ga Jaridar INDA RANKA inda ya ce, “Wannan mataki na daga cikin kokarin hukumar wajen yaki da safarar kayan maye a jihar Kano.”
Ya ce, jami’an Hisbah sun shigo da motar cikin ofishinsu inda suka adana kayan, sannan kuma tuni aka fara bincike tare da shirin gurfanar da waɗanda ake zargi da hannu cikin lamarin a gaban kotu.
Ya kuma ce, hukumar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta ba tare da gajiyawa ba, yana mai jan kunnen masu aikata laifukan da su daina ko kuma su fuskanci hukunci.
Hukumar Hisbah dai na daga cikin hukumomin da ke sa ido kan aikata abubuwan da ke sabawa dokokin addini a jihar Kano, ciki har da hana sayarwa da kuma shan giya.
