News
Gwamnatin Kano Ta Bukaci Jami’an Hulɗa Da Jama’a Su Yi Amfani Da Shaidar NIPR Wajen Inganta Ayyukansu
Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci dukkan jami’an hulɗa da jama’a (PROs) da aka tabbatar da su a matsayin membobin ƙungiyar ƙwararrun masu hulɗa da jama’a ta ƙasa (NIPR) da su yi amfani da wannan dama wajen inganta ayyukansu da kuma samun ƙarin maki a aikinsu na yau da kullum.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan yayin bikin rantsar da jami’an hulɗa da jama’a daga ma’aikatu, hukumomi da ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Rundunar Sojin Sama Ta Kai Hari Gurin Shagalin Auren Yan Bindiga A Zamfara
Kwamishinan ya ce samun shaidar ƙwarewar NIPR ba wai kawai wata alama ce ta cancanta ba, har ila yau wata dama ce da za ta bai wa jami’an damar ƙara kuzari da inganci a harkokinsu na yaɗa labarai da sadarwa tsakanin gwamnati da al’umma.
Ya kuma jinjinawa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa goyon bayan da ya bayar wanda ya sa aka ɗauki nauyin horar da jami’ai 71 da kuma tabbatar da su a matsayin mambobin ƙungiyar NIPR.
“Wannan wani babban ci gaba ne da zai ƙara ma’aikatan mu kwarin guiwa da kuma buɗe musu ƙofofin ci gaba a aikinsu,” in ji Waiya.
Wasu daga cikin jami’an da suka samu shaidar ƙwarewar sun bayyana farin cikin su da kuma godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan dama ta musamman da aka ba su.
A cewarsu, samun horo da shaidar NIPR wata babbar dama ce da za ta haɓaka ƙwarewa, ƙarfafa sadarwa da kuma ƙara fahimta tsakanin gwamnati da jama’a a matakai daban-daban.
Daga cikin mutane 83 da suka yi rijista domin samun shaidar NIPR, gwamnati ta dauki nauyin mutum 71.
