Connect with us

News

Jami’an Hukumar EFCC Sun Tsare Aminu Waziri Tambuwal, Tsohon Gwamnan Sokoto 

Published

on

FB IMG 1754942234739

Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) na tsare da kuma binciken tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal, a Abuja kan zargin cire kuɗaɗe ba bisa ka’ida ba har naira biliyan 189.

Majiyoyi daga hukumar sun ce cire kuɗaɗen sun saba wa dokar hana almundahana ta kuɗi (Money Laundering Prevention & Prohibition Act, 2022).

Mutumin Da Ake Zargi Da Ajalin Jami’in Civil Defence Ya Rasu A Hannun Hukumar A Jigawa

Ba a tabbatar da lokacin da aka yi wadannan cire-cire ba a halin yanzu.

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamnan ya isa hedikwatar EFCC da misalin ƙarfe 11:30 na safe, inda ake masa tambayoyi kan zargin almundahana.

Tambuwal ya shugabanci Jihar Sokoto daga 2015 zuwa 2023, kuma ya taba zama Kakakin Majalisar Wakilai daga 2011 zuwa 2015.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ki yin bayani kan lamarin lokacin da aka tuntube shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending