Connect with us

News

Aikin Jarida Na Bukatar Gogewa Da Kwarewa – Gwamnatin Kano

Published

on

NUJ Logo (1)

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Ayyukan Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Abdullahi Ibrahim Waiya, ya bayyana aikin jarida a matsayin muhimmin fanni da ke bukatar cikakkiyar gogewa da samun ƙwarewa a aikace domin yaɗa labarai masu inganci da nagarta ga al’umma.

Ya bayyana hakan ne a yayin wani taron musamman da ƙungiyar Ƴan Jarida ta Kasa (NUJ) reshen Kano tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Ayyukan Cikin Gida suka gudanar a birnin Kano, wanda aka shirya da sahalewar Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Advertisement

Shugaban Tinubu Zai Ziyarci Ƙasashe  Uku

A cewarsa, gwamnatin jihar ta kuduri aniyar ci gaba da bai wa matasa ƴan jarida horo na gani da ido da kuma koyarwa ta musamman domin ƙara musu basira da kwarewa a sana’ar jarida, tare da samar da yanayi mai kyau da zai taimaka wajen bunƙasa harkar.

A nasa jawabin, Shugaban NUJ na ƙasa, Comrade Alhassan Yahaya, ya bayyana farin cikinsa bisa yadda taron ya gudana, yana mai cewa ya kunshi tattaunawa kan batutuwan da suka shafi inganta albashin ƴan jarida, samar musu da kariya ta fannin inshorar lafiya, da kuma ci gaba da horas da su domin inganta aikin jarida a fadin ƙasar.

Advertisement

Ya yi kira ga mambobin NUJ a Kano da su yi rajista da shirin inshorar lafiya, domin inganta lafiyarsu da ta iyalansu.

Haka kuma, ɗaya daga cikin gogaggun ƴan jarida a jihar, Ahmad Aminu, ya bayyana cewa taron ya samar da muhimman hanyoyi da dabaru da za su taimaka wajen ɗaukaka harkar jarida, tare da ƙara damarmaki ga masu aikin domin samun horo na zamani.

Advertisement

Taron ya samu halartar fitattun masana harkar jarida, tsofaffin kwamishinonin yaɗa labarai da ayyukan cikin gida, ciki har da Baba Haliru Dantiye da Farfesa Umar Faruk Jibrin, da kuma sauran jami’ai da manyan baki na musamman.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending