News
‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 107, Sun Kwato Muggan Makamai Da Miyagun Kwayoyi A Kano
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta samu gagarumar nasara wajen magance laifuka a jihar, musamman ta hanyar sabon tsarinta na Operation Kukan Kura.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, ya bayyana haka ne a yayin taron manema labarai da aka gudanar a helkwatar rundunar dake Bompai, inda ya ce tsarin ya taimaka sosai wajen rage yawan fadan ‘yan daba da sauran miyagun laifuka a Kano.
Gwamnatin Tarayya Musanta Zargin Da El-rufai Ya Yi Kan Biyan Kuɗi Ga ’Yan Bindiga
“Tun bayan kaddamar da Operation Kukan Kura a ranar 1 ga watan Yuli, 2025, rundunar ta kwato muggan makamai 473 tare da miyagun kwayoyi masu tarin yawa,” in ji shi.
A cewar rundunar, a cikin watan Agusta 2025 kadai, an kama mutane 107 da ake zargi da aikata laifuka iri daban-daban, ciki har da ‘yan fashi da makami, masu safarar miyagun kwayoyi, barayin motoci, ‘yan daba da sauransu.
Bayanan Wadanda Aka Kama, ‘Yan fashi da makami: 8, Masu garkuwa da mutane: 8, Masu safarar mutane: 3, Masu safarar miyagun kwayoyi: 14, Barayin motoci: 2, Barayin babura: 6, Sauran barayi: 5, ‘Yan daba: 61.
Wanda Aka Ceto Mutum daya daga hannun masu safarar mutane.
Kayan Da Aka Kwato, Bindiga kirar AK-47 guda 1, bindigogi kirar gida guda 7, harsashi guda 11, Motoci 8, babura 8, shanu 8, Adduna 102, wukake 74, Sinkin tabar wiwi 111, daurin wiwi 458, Robobin sholisho 211, kwalaben sukurdaye 257, Kwayoyin exol (5 fakiti, 21 tsaba), diazepam (20 fakiti, 13 tsaba), Sinkin shaddar Kampala 44, Wayoyin hannu 59, POS guda 3, Katin cire kudi na Opay 17, Da sauran kayan shaida.
Kwamishinan ya yaba wa al’ummar Kano bisa hadin kai da bayanan sirri da suke bayarwa, wanda ya ce hakan ya taimaka sosai wajen dakile laifuka.
“Ina kira ga jama’ar Kano da su ci gaba da bamu hadin kai, su rika sanar da mu duk wani abu da ke da zargi ta ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kuma ta lambobin waya da muka bayar,” in ji shi.
