News
Sama Da Mutum Miliyan 3.5 Ne Suka Yi Rijistar Katin Zaɓe Ta Yanar Gizo – INEC
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce sama da ‘yan Najeriya miliyan uku da dubu dari biyar (3.5m) ne suka yi rijistar katin zaɓe ta yanar gizo cikin makonni uku kacal da fara aikin.
A sanarwar da kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Sam Olumeku, ya fitar ranar Litinin, ya ce jimillar 3,544,850 ne suka kammala rajista daga ranar 18 ga watan Agusta zuwa 7 ga Satumba.
Sanarwar ta nuna cewa daga cikin waɗanda suka yi rajistar, 1,709,933 (48.24%) maza ne, yayin da 1,834,917 (51.76%) mata ne.
Mafi yawan masu rijistar kuwa matasa ne ‘yan shekaru 18 zuwa 34, waɗanda suka kai 2,291,809 (64.65%). Haka kuma, 882,441 (24.89%) daga cikinsu dalibai ne.
INEC ta bayyana cewa nan gaba za ta wallafa cikakkun alkaluma kan waɗanda suka yi rijistar ta yanar gizo da kuma waɗanda suka je cibiyoyin rajista.
Hukumar ta kuma yaba da irin goyon bayan da ƙungiyoyi da al’umma suka bayar wajen wayar da kai, sai dai ta sake jaddada cewa ‘yan Najeriya masu shekaru 18 zuwa sama ne kaɗai suka cancanci yin rijistar katin zaɓe.
