Connect with us

News

Ranar Masu Fama da Cutar Laka: Gwamnatin Kano da Kungiyoyi Sun Jaddada Muhimmancin Tallafi

Published

on

IMG 20250921 WA0022

DAGA SAFIYA MUHAMMAD USMAN

An gudanar da bikin Ranar Masu Fama da Cutar Laka ta Duniya a ranar 20 ga Satumba a Kano, inda aka tattauna hanyoyin tallafawa masu fama da cutar da kuma matakan kariya ga al’umma.

Advertisement

Taron, wanda ya gudana da haɗin gwiwar ƙungiyoyin masu fama da cutar da ma’aikatar kula da mata, kananan yara da masu bukata ta musamman, ya samu halartar wakilai daga gwamnati, masana a fannin lafiya, kungiyoyi masu zaman kansu da kuma masu fama da cutar.

NDLEA Ta Cafke ’Yan Najeriya Biyu Da Suka Dawo Daga Brazil Da Hodar Iblis Da Koken

Kwamishiniyar mata, kananan yara da masu bukata ta musamman a jihar Kano, Hajiya Amina Sani Abdullahi, ta tabbatar da cewa gwamnatin Kano na ɗaukar matakai don inganta rayuwar masu bukata ta musamman. Ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin kafa hukumar da za ta kula da su nan ba da jimawa ba.

Advertisement

Shugaban Ƙungiyar Masu Fama da Cutar Laka, Malam Abdurrahman Uba Daushe, ya bayyana farin cikinsu da tunawa da wannan rana. Ya ce taken bana shi ne “A guji faɗuwa”, yana mai jaddada irin kalubalen da suke fuskanta. Ya kuma yaba wa gwamnatin Kano bisa rabon kayayyakin tallafi ga masu fama da cutar.

A nasa bangaren, babban likita a Asibitin Koyarwa na Jigawa, Dr Abubakar Musa Ringim, ya yi kira ga direbobi da sauran jama’a da su riƙa kula da kansu a kan hanya don gujewa haɗurra da ke iya jawo cutar Laka.

Advertisement

Shugaban Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, Hon. Sani Ahmed Mai Rago, ya ce gwamnati na ƙoƙari wajen inganta rayuwar masu bukata ta musamman. Ya yi kira ga masu hannu da shuni da su shiga cikin sha’anin tallafa musu, musamman wajen lafiyar su.

Shi ma a nata bangaren, shugabar ƙungiyar kare haƙƙin tsofaffi da masu bukata ta musamman, Hajiya Rabi Yusuf Gezawa (MON), ta bayyana cewa masu fama da cutar Laka suna cikin rukunin da ke fuskantar matsananciyar wahala a rayuwa. Ta yi kira da a daina kiransu da masu “nakasa” kai tsaye domin hakan na rage darajarsu a idon jama’a.

Advertisement

Wasu daga cikin masu fama da cutar da suka amfana da tallafin da aka raba sun nuna jin daɗi, inda suka yaba wa gwamnatin Kano bisa rabon kayayyakin da suka haɗa da kekunan guragu da auduga ta musamman da sauran kayan amfani.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending