News
Mutane 7 Sun Rasa Rayukansu, 67 Sun Kamu da Cutar Fata A Adamawa
Wata sabuwar cutar fata ta jefa al’ummar ƙauyen Malabu cikin fargaba a Jihar Adamawa, inda ta yi sanadin mutuwar mutane bakwai, yayin da wasu 67 suka kamu da ita.
Jami’an Lafiya na Gwamnatin Tarayya sun fara gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin cutar. Kodinetan riƙo na shirin kula da cutukan tarin fuka, fata da sanyi mai tsanani, Dakta Adesigbin Olufemi, ya tabbatar da al’amarin a wata hira da manema labarai ranar Lahadi.
A cewarsa, tun daga ranar 10 ga watan Satumba, an samu tabbacin mutane 68 sun kamu da cutar, inda takwas daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali a Asibitin Koyarwa na Modibbo Adama, Yola.
Cutar, wadda ke haifar da ƙuraje masu fashewa da lalata fata da ƙasusuwa, ta jefa al’ummar Malabu cikin tashin hankali.
Binciken farko ya nuna cewa cutar ta samo asali ne daga Gambon Fatar Jiki wato Buruli Ulcer, wadda aka fi samun ta a yankunan ruwa. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce gano cutar da wuri na taimakawa wajen rage yaduwa da haɗarin mutuwar mutane.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
