Connect with us

News

Jami’an KAROTA Sun Kama Kayan Da Aka Sace A Makarantar  Gwamnati Na Fiye Da Naira Miliyan 80 

Published

on

Kotu Ta Ja Kunnen Jami,an  KAROTA Akan Yanda Suke Gudanar Da Aikinsu

Jami’an Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) sun dawo da kayan ICT masu aiki da hasken rana da aka sace daga Makarantar Sakandaren ’Yan Mata Aisha Shehu, dake Kuka a karamar hukumar Fagge na fiye da Naira miliyan 80.

‎Babbar malamin makarantar, Hajiya Rufa’atu Mahmud Baffa, ta bayyana cewa barayin sun kutsa cikin dakin ICT na makarantar, inda suka cire bangon rufi da kayan solar  sannan suka dauki kwamfutoci da sauran na’urorin zamani. Sai dai, jami’an KAROTA da ke sintiri da daddare sun gano kayan a wani wuri, inda barayin suka tsorata suka tsere.

Advertisement

Saudiyya Ta Naɗa Sabon Babban Mai Bada Fatawa Na Ƙasar

‎Daraktan Gudanarwa na KAROTA, Hon. Faisal Mahmud Kabir, ya yaba wa jami’an hukumar bisa jajircewa da kishin kasa, inda ya tabbatar da cewa duk kayan da aka sace an dawo da su gaba ɗaya, kuma an mika su ga makarantar. Ya ce duk da barayin sun tsere, an samu nasarar kare dukiyar makarantar.

‎Kabir ya jaddada bukatar kara inganta tsaro a makarantu, musamman wadanda ke cikin shirin AGILE da Bankin Duniya ke tallafawa, domin ci gaba da bunkasa bangaren ilimi a jihar Kano.‎

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILY POST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending