News
Gwamna Kano Ya Miƙa Korafe-korafen Kungiyoyin Addini Kan Malam Lawan Triumph Zuwa Ga Majalisar Shura
Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya karɓi korafe-korafen da wasu kungiyoyin addinin Musulunci suka gabatar dangane da karatun da Malam Lawan Triumph ya gudanar. Gwamnan ya mika korafe-korafen zuwa Majalisar Shura ta Jihar domin yin nazari da daukar mataki.
A cikin wata sanarwa, Sakataren Yada Labarai na Gwamnatin Jihar Kano, Musa Tanko, ya bayyana cewa an samu korafe-korafen daga kungiyoyi da dama, ciki har da:
Tsoffin Ƴan Sanda Za Su Sake Gudanar Da Babbar Zanga-Zanga A Gaban Majalisar Dokoki
Safiyatul Islam of Nigeria
Tijjaniya Youth Enlightenment Forum
Interfaith Parties for Peace and Development
Sairul Qalbi Foundation
Habbullah Mateen Foundation
Imams of Juma’at Mosques under Qadiriyya Movement
Committee of Sunnah Preachers, Kano
Multaqa Ahbab Alsufiyya
Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya tabbatar da cewa takardun korafe-korafen sun mika zuwa Majalisar Shura domin ta yi cikakken nazari.
Korafe-korafen sun biyo bayan zanga-zangar da wasu kungiyoyin addini suka gudanar a Kano a jiya, inda suka nuna damuwa kan karatun Malam Lawan Triumph. Kungiyoyin sun ce malamin ya ketare hurumin wasu malamai, yayin da gwamna ya bukaci su kawo korafensu a rubuce domin daukar mataki.
