News
Sama Da Ƙoda 651 Aka Siyar Ba Bisa Ƙa’ida Ba a Nijeriya
An gano yadda talauci da matsin tattalin arziki ke tura daruruwan ‘yan Nijeriya zuwa sayar da ƙodarsu, yayin da rahotanni suka nuna cewa sama da ƙoda 651 aka siyar da su ba bisa ƙa’ida ba tsakanin shekarar 2015 zuwa 2020, tare da samun kimanin dala biliyan 41 a kasuwar fataucin gaɓoɓi ta ɓoye.
Farfesa Aliyu Abdu, babban likitan nephrologist a Jami’ar Bayero Kano (BUK), ya bayyana hakan a wani taron ƙara wa juna sani da aka gudanar a Abuja, inda ya bayyana wannan kasuwanci a matsayin wata ƙazamar sana’a ta duniya da ke haɗa dillalai, likitoci, ’yan damfara da mutanen da ke neman fita daga talauci.
Yadda Ganduje Ya Musanya Hannun Jarin Gwamnatin Kano A Tashar Dala Da Kamfanin Ƴaƴansa
Ya ce, waɗannan ’yan kasuwar sassan jiki suna haɗa masu son siyar da ƙodarsu da masu kuɗi, suna mai da talauci hanya ta kasuwanci don tara riba. Duk da cewa Dokar Kiwon Lafiyar Nijeriya ta 2014 ta haramta sayar da gaɓoɓi tare da hukunta masu aikata laifi, raunin aiwatar da doka ya bai wa kasuwar bayan fage damar bunƙasa.
Rahotanni sun nuna cewa a duk shekara ana sayar da ƙoda sama da 10,000 a duniya ba tare da kulawa da lafiyar masu siyar da su ba, abin da ke barin su cikin raunin lafiya, matsin kuɗi da damuwa. Lamarin ya haɗa da manyan mutane, ciki har da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu, wanda aka same shi da laifin safarar ƙoda zuwa Burtaniya.
A shekarar 2021, wani asibiti a Abuja sai da ya sanya rubutun “Ba Mu Sayi Ƙoda!” bayan tarin mutanen da suka nemi siyar da sassan jikinsu saboda matsin tattalin arziki bayan annobar Korona.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
