News
Yadda Matar Wani Soja Ta Cinna Masa Wuta Ya Mutu
Wani soja mai muƙamin Laftana a rundunar sojan Najeriya, Samson Haruna, ya mutu bayan da matarsa ta cinna masa wuta a lokacin da suka samu sabani a gida.
Lamarin mai cike da firgici da tausayawa ya faru ne a ranar 22 ga Satumba, 2025, a Wellington Bassey Barracks da ke Ibagwa, ƙaramar hukumar Abak, a jihar Akwa Ibom.
Rahotanni sun bayyana cewa matarsa, Mrs. Samson Haruna, ta watsa masa fetur sannan ta kunna masa ashana a lokacin da suke cikin zafafan maganganu a gida. Wannan ne ya haifar da mummunar ƙonewa a jikinsa gaba ɗaya.
Wata majiya ta tsaro ta shaida wa masani kan batutuwan tsaro a Najeriya, Zagazola Makama, wanda ya wallafa labarin a shafin sa na X (wanda ake kira Twitter a da), cewa marigayin wanda kuma likita ne a 6 Battalion Regimental Medical Office (RMO), an garzaya da shi asibiti bayan samun mummunar ƙonewa.
“An fara ba shi kulawar gaggawa a Military Reference Section (MRS) da ke cikin barikin, kafin daga bisani a tura shi zuwa University of Uyo Teaching Hospital don ƙarin jinya,” in ji majiyar.
Sai dai duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi don ceto ransa, Laftana Haruna ya mutu sakamakon raunin ƙonewar da ya samu.
Hukumar tsaro ta tabbatar da cewa an kama matar, kuma tana hannun jami’an tsaro yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
