News
Wata Mace Ta Rabu Da Mijinta Saboda Kin Gyara Mata Wayarta Da Ta Lalace
Wata mata mai suna Zainab Alhassan ta nemi rabuwa da mijinta Tijjani Muhammad a kotu saboda ya ƙi gyara mata wayarta da ta lalace, wadda ta ce darajarta ta kai N70,000.
Zainab ta shaida wa kotun Shari’a cewa ta gaji da zaman auren, kuma tana son a sake ta ta hanyar Khul’i – wato irin sakin da mace ke maido wa mijinta sadakinta domin ta samu ’yancin kanta.
“Na gaji da wannan aure, kuma bana son ci gaba da zama da shi. Na shirya in maido da sadakin da ya bani domin in sami ’yanci na,” in ji ta.
Ta ce tana kallon fim a wayarta lokacin da mijinta ya fara faɗa da ita, inda ya karɓi wayar ya buga ta ƙasa har ta lalace. Duk da haka, ta amsa cewa ba ta da wata shaida da za ta tabbatar da wannan zargi.
A nasa ɓangaren, mijin, Tijjani Muhammad, ya shaida wa kotu cewa bai da matsala da buƙatar sakin da matarsa ke nema, sai dai ya musanta zargin cewa shi ne ya lalata wayar.
Bayan sauraron ɓangarorin biyu, Alƙali Mu’awiyya Shehu ya yanke hukunci da raba auren bisa tsarin Khul’i, inda Zainab za ta mayar da sadakin N30,000 da ta karɓa.
Sai dai kotun ta ƙi amincewa da buƙatar da Zainab ta nema ta biya ta kuɗin wayar da ta ce mijin ta ya lalata.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
