News
Gidauniyar Dr Aminu Magashi Garba Na Ci Gaba Da Tallafa Wa Asibitocin Kano Da Magunguna
DAGA SAFIYA MUHAMMAD USMAN
Gidauniyar Dr Aminu Magashi Garba ta ci gaba da shirin bada tallafin magunguna duk karshen wata ga marasa lafiya a asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake Kano.
Tallafin na gudana ne tare da haɗin gwiwar kungiyoyin Yospis, CHR, Kano Health Care Four Room, V-PeSDI, da wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu.
NDLEA Ta Kama Ɗan Kasuwa Da Ya Ɓoye Koka’in A Gabansa A Filin Jirgin Saman Kano
Da yake jawabi yayin taron bada tallafin, Dr Aminu Magashi Garba ya ce kula da lafiyar jama’a, musamman masu ƙaramin ƙarfi, babban al’amari ne da ke buƙatar kulawa ta musamman.
“Lafiya ce ginshiƙin rayuwa. Mutum ba zai iya gudanar da ayyukan yau da kullum ba sai da lafiya. Wannan ne ya sa muka ɗauki nauyin tallafawa marasa galihu, tare da goyon bayan Gwamnatin Jihar Kano a fannin lafiya,” in ji Dr Magashi.
Ya ƙara da cewa gidauniyar za ta ci gaba da kai magunguna na kimanin naira dubu dari biyu (₦200,000) duk karshen wata ga asibitin Murtala Muhammad da kuma asibitin Abdullahi Wase dake Kano.
Shugabar sashen masu buƙatar gaggawa na asibitin Murtala Muhammad, Metron Hasana Suleiman, ta yaba da wannan kokari na gidauniyar.
“Tallafin magungunan nan yana taimaka mana matuƙa wajen kula da marasa lafiya da ake kawo da gaggawa. Sau da dama muna samun karancin magunguna, amma wannan tallafi yana cike gibin,” in ji Metron Hasana.
A ƙarshe, taron bada tallafin ya samu halartar Shugabar Kungiyar CHR, Hajiya Nafisa Shehu Ibrahim, da Shugabar Kungiyar Yospis, Zainab Nasir, tare da wasu wakilan ƙungiyoyi masu zaman kansu.
