Connect with us

News

Yadda Wani Mahaukaci Ya Farmaki Jama’a, Ɗaya Ya Mutu Uku Sun Jikkata

Published

on

1 15 1

Rahotanni daga jihar Taraba na cewa wani mutum da ake zargin yana da tabin hankali ya kashe mutum ɗaya, ya kuma jikkata wasu uku a garin Buzzah, da ke cikin ƙaramar hukumar Zing, a daren Asabar.

Wani mazaunin garin da ya ga yadda abin ya faru ya ce, mutumin da ake kira Denis, wanda aka saba ganin yana yawo a cikin garin Zing sanye da farin kaya yana yin kamar mai wa’azi, ne ya kai harin ne da  misalin ƙarfe 11:00 na dare.

Advertisement

Ma’aurata 136 Sun Kashe Juna Sakamakon Rikici A Cikin Shekaru 4 A Najeriya 

An ce lokacin da abin ya faru, Denis ya kai hari kan mutane hudu, inda Hammanyaro Cha’ayonli ya mutu nan take, yayin da sauran uku suka samu munanan raunuka.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa biyu daga cikin wadanda suka jikkata ‘yan banga ne da suka taɓa dakatar da motsin Denis saboda tsoron halayensa.

Advertisement

Wani daga cikin mazauna garin ya ce, “Yana ganin waɗanda ya farmaka a matsayin masu barazana, saboda suna hana shi yin yawo barkatai.”

Majiyoyi daga yankin sun ce Denis yana yawan yawo da ƙaramin makami, abin da ya jefa al’umma cikin fargaba kafin ma wannan harin ya faru.

Advertisement

A yanzu haka, wadanda suka jikkata na karɓar magani a asibitin Zing General Hospital, yayin da jami’an tsaro suka fara bincike don gano abin da ya haifar da harin da kuma matakin da za a ɗauka.

 

Advertisement

DAILY POST

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending