News
Ma’aikatar Muhalli Ta Dakatar da Rangwamen Izini Ga Masana’antu A Kano
Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta dakatar da bayar da rangwamen izini ga masana’antu, tare da soke duk wani rangwamen da aka riga aka bayar.
Kwamishinan ma’aikatar, Dr. Dahiru Muhammad Hashim, ya bayyana haka a ofishinsa a yau, bayan karɓar rahoto da ya nuna cewa wasu kamfanoni na karya doka ta hanyar ci gaba da aiki a lokacin da aka ware don ayyukan tsaftace muhalli da kuma takunkumin zirga-zirga.
Ƙungiyar One Kano Agenda Ta Yi Fatali Da Shirye-shiryen Zanga-zangar Neman Sakin Nnamdi Kanu A Kano
Dr. Hashim ya jaddada cewa ma’aikatar ba za ta lamunci kowanne irin hali da zai kawo cikas ga manufofinta na asali ba. Ya ce an dauki wannan mataki ne domin sake duba tsarin manufofin muhalli na yanzu, daidaita su da nagartattun hanyoyin aiki, da kuma bayar da jagora ga jama’a kan yadda za su mu’amala da muhalli.
Kwamishinan ya yi kira ga dukkan masana’antu, gwamnati da masu zaman kansu, da su nuna kishin kasa ta hanyar goyon bayan shirye-shiryen raya muhalli na gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da kauce wa duk wani yunƙuri da zai kawo koma-baya ga ci gaban jihar da kuma jure sauyin yanayi.
