Connect with us

News

Babban Taron Jami’yyar APC: Yadda Ƴan APCn Kano su ka dawo ‘Hannu Wofi

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

A jiya Asabar jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya da jihar Kano ta kammala babban taron ta na ƙasa inda ƴan takarar shugabancin jam’iyyar su ka amince tare da barwa tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu ragamar shugabancin jam’iyyar.

Haka kuma wakilai fiye da 7,000 ne su ka kaɗa ƙuri’unsu wajen zaɓar sauran muƙaman da su ka rage a cikin jam’iyyar.

Sai dai wani abin mamaki shi ne yadda aka zaɓi muƙamai daban-daban a cikin jam’iyyar ta APC ba tare da wani ɗan jihar Kano ya kai ga nasarar samun wani muƙami ko ɗaya ba. Duk da cewa jihar Kanon babbar jiha ce da jam’iyyar APC ɗin ta daɗe tana nanata tasirinta a siyasar Najeriya.

Advertisement

Haka kuma wannan yana zuwa ne a lokacin da ake yiwa jihar Kanon kirari da ‘Kano ta dabo tumbin Giwa, ko da me ka zo an fika, wanda hakan ne ya sa ake ganin ita ce cibiyar siyasar Arewacin Najeriya, la’akari da irin fitattun ƴan siyasar da su ka fito daga jihar kuma muryarsu ta yi tasiri a al’amuran siyasar Najeriya.

Su wanene sababbin shugabannin jam’iyyar APC?

Jim kaɗan da kammala babban taron Gwamnan jihar Jigawa Muhammadu Badaru Abubakar ya sanar da sunan Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban jam’iyyar ta APC. Sauran shugabannin sun haɗa da:

  • Abubakar Kyari – Mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar Arewa.
  • Ema Enaukwu – Mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar Kudu.
  • Otunba Omisore – Sakataren jam’iyya.
  • Festus Fuanter – Mataimakin Sakataren jam’iyya.
  • Muhazu Rijau – Mataimakin shugaban jam’iyyar mai kula da shiyyar Arewa ta Tsakiya.

Mustapha Salihu – Mataimakin shugaban jam’iyyar mai kula da shiyyar Arewa maso Gabas.

  • Salihu Lukman – Mataimakin shugaban jam’iyyar shiyyar Arewa maso Yamma.
  • Ijeoma Arodiogwu – Mataimakin shugaban jam’iyyar shiyyar Kudu maso Gabas.
  • Victor Giadom – Mataimakin shugaban jam’iyyar shiyyar Kudu maso Kudu.
  • Isaac Kekemeke – Mataimakin shugaban jam’iyyar shiyyar Kudu maso Yamma.
  • Ahmed El-Marzuk – Mashawarcin jam’iyyar ta fuskar Shari’a.
  • Uguru Ofoke – Ma’ajin Jam’iyya.
  • Bashir Gumel – Sakataren kuɗi na jam’iyya.
  • Suleiman Argungun – Sakataren tsare – tsare.
  • Betta Edu – Shugabar Mata.
  • Abdullahi Israel – Shugaban Matasa.
  • Tolu Bankole – Shugaba na Musamman.
  • F.N Nwosu – Sakataren Walwala.
  • Felix Morka – Kakakin Jam’iyya.
  • Abubakar Maikafi – Mai Binciken Kuɗi.
  • Ibrahim Salawu – Mataimakin Sakataren Shari’a.
  • Omorede Osifo – Mataimakin Ma’aji.

Su waye su ka nemi shugabanci a APC daga Kano?

A cikin ƴan jihar Kano da su ka fito neman shugabanci a cikin jam’iyyar a matakin ƙasa akwai irinsu Musa Mujahid Zaitawa da Amb. Rasheeda Abdullahi Mai Sa’a da kuma Barrister Isma’il Ahmed Buba.

Sai dai Barrister Isma’il Ahmed Buba wanda babban mai bai wa shugaba Buhari shawara kan shirin tallafa wa al’umma, ne kawai ya samu kaiwa ga shiga zaɓe duk da rashin nasarar da ya yi a hannun Suleiman Argungun wanda ya fito daga jihar Kebbi.

Laifin waye?

Advertisement

Tuni dai masu sharhi akan al’amuran yau da kullum su ke ɗora alhakin faruwar hakan ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, saboda rashin matsawa wajen ganin ya marawa ɗan jiharsa baya a muƙamin da ya fito nema.

Wani lauya mai zaman kan sa da ke Kano, Barrister Lawan Yaro ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Facebook akan yadda Kanawa su ka rasa samun ko kujera ɗaya a shugabancin APC ɗin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending