News
Tirela Ta Murkushe Yaran Mota Har Lahira
Wani Yaran mota ya rasa ransa a daren Laraba a yankin Ogolonto da ke Ikorodu, bayan da wata babbar motar ɗaukar kaya ta murkushe shi yayin da take motsi.
Lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 11 na dare, kuma hukumomin tsaro sun ce ana ci gaba da binciken yadda ya faru.
TALLAFIN GWAMNATI: Kashi 44 cikin 100 Ne Kaɗai Ke Isa Ga Masu Buƙata A Najeriya —Rahoto
Shaidu a wurin sun ce matashin ya faɗa a ƙarƙashin motar ne yayin da yake ƙoƙarin daidaita motar ɗauke da kaya, inda tayoyin motar suka bi ta jikinsa, suka kashe shi a nan take.
Shugaban Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Lagos (LASTMA), Olalekan Bakare-Oki, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce jami’an rundunar “Special Night Patrol Team” ta LASTMA sun kama direban motar.
A cewar Bakare-Oki, binciken farko ya nuna cewa marigayin ya sauko daga motar domin sanya katako a ƙarƙashin tayoyi saboda matsalar birki. Sai dai a yayin wannan yunƙuri ne ya zame ya faɗa, motar kuma ta murkushe shi.
-
News22 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
-
News2 days ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
