News
Gwamnatin Tarayya Ta Ceto Daliban Da Aka Sace a Kebbi
An sake samun sabon labari mai dadi daga Jihar Kebbi, inda rahotanni suka tabbatar da cewa dalibai mata 24 da aka sace daga Government Girls Secondary School Maga, a Karamar Hukumar Danko/Wasagu, sun kubuta. gwamnatin tarayya ta tabbatar da ceto su a ranar Talata, 25 ga Nuwamba 2025.
Mai Ba wa Shugaban Kasa Shawara Kan Bayanai da Tsare-Tsare, Bayo Onanuga, shi ne ya tabbatar da kubutar daliban cikin sanarwar da ya fitar, yana mai cewa jami’an tsaro sun gudanar da aikin hadin gwiwa domin ganin an dawo da su cikin koshin lafiya. Har yanzu ba a bayyana ko an biya kudin fansa ba ko kuma an kama wadanda suka yi garkuwa da su.
Kotu Ta Yanke Wa Magidanci Hukuncin Daurin Shekara Daya Saboda Satar Wake kwano Daya
Kakaki24 ta tattaro cewa har yanzu iyaye da al’ummar yankin na jiran karin bayani daga hukumomi, musamman game da yadda aka ceto daliban da kuma matakan da gwamnati ke shirin dauka don dakile irin wannan lamari a gaba. A kwanakin baya an yi ta korafe-korafe kan karuwar hare-haren ‘yan bindiga a yankunan Arewa maso Yamma, wanda ke haifar da tsoro da katse harkokin ilimi.
Sai dai ana sa ran gwamnatin jiha da ta tarayya za su fitar da cikakken bayani nan gaba, yayin da al’umma ke nuna godiya bisa kubutar daliban ba tare da samun rahoton mutuwa ba. Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake ci gaba da kira ga gwamnati ta kara kaimi wajen kare makarantu da dalibai a yankunan da ke fuskantar barazana.
