Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Ceto Fasinjoji 21 Da Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su A Kogi

Published

on

0933fc35 a2a5 4edb 833e 72e8ec6cdd4a

Jami’an tsaro a jihar  Kogi sun kubutar da fasinjoji 21 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su, bayan harin da aka kai kan motoci da dama a manyan hanyoyin jihar. A yayin harin, jami’an tsaro biyu — soja guda ɗaya da wani mai sa kai — sun rasa rayukansu.

Rahotanni sun bayyana cewa kusan ’yan bindiga 100 ne suka tare jerin motocin fasinja, ciki har da Toyota Sienna daga Oshogbo zuwa Kaduna, Toyota Hiace daga Owo zuwa Abuja, wata Hiace daga Abuja zuwa Ekiti, da Toyota Carina daga Lokoja zuwa Kabba.

Advertisement

Ƙungiyar Likitoci Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Tsunduma 

Hakanan, wata motar Dangote mai ɗauke da buhunan siminti da wata motar J5 cike da barkono daga Kano zuwa Lagos sun tsinci kansu cikin harin.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana, inda fasinjoji suka shiga firgici, wasu daga cikinsu kuma aka yi ƙoƙarin yin garkuwa da su.

Advertisement

Rundunar haɗin gwiwa ta musamman wadda ta ƙunshi Sojojin Brigade ta 12, sashen Quick Response, jami’an NSCDC, da mafarauta da masu sa kai, ta bi ’yan bindigar cikin daji. An yi musayar wuta mai zafi, lamarin da ya kai ga ceto mutum 21 — ciki har da jaririya ’yar kwana tara a duniya.

 

Advertisement

ZAGAZOLA MAKAMA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending