Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 7 Da Aka Sace A Kano

Published

on

1764505831082

Rundunar Sojin Najeriya karkashin Operation MESA ta ce ta ceto mutane 7 da aka sace a kauyen Yankamaye Cikin Gari da ke karamar hukumar Tsanyawa a jihar Kano.

A cewar sanarwar da Capt. Babatunde Zubairu, Mataimakin Daraktan Harkokin Yada Labarai na Rundunar Soji (3 Brigade), harin ya faru ne a daren ranar 29 ga Nuwamba, da misalin karfe 11 na dare.

Advertisement

An Hallaka Mutane 4, An Jikkata 10 Yayin Gudanar Da Shagalin Bikin ‘Birthday’

Capt. Zubairu ya ce an samu kiran agaji cewa wasu ‘yan bindiga masu yawa sun kai hari kauyen, sun hallaka wata mata mai shekaru 60 tare da sace mutane 10.

“Rundunar soji tare da jami’an ‘yan sanda suka tura tawaga zuwa wajen, inda suka bi sawun ‘yan bindigar zuwa kauyen Rimaye,” in ji Capt. Zubairu.

Advertisement

Ya kara da cewa sojojin sun yi musayar wuta da maharan, inda suka samu nasarar ceto mutane 7 daga cikin wadanda aka sace, yayin da ‘yan bindigar suka tsere zuwa karamar hukumar Kankia a jihar Katsina.

 

Advertisement

NAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending