News
KANO: Ba A Samu Asarar Rai Ba A Gobarar Da Ta Tashi A Babban Asibitin Rogo
Shugaban Karamar Hukumar Rogo, Alhaji Abubakar Mustapha Rogo, ya ce babu wanda ya rasa ransa a gobarar da ta tashi a wani bangare na Babban Asibitin Rogo da ke jihar Kano.
A cewar sa, gobarar ta haifar da ɗan razana ga marasa lafiya da ma’aikatan jinya, kafin jami’an kashe gobara da mazauna yankin su shawo kan ta.
Jami’in Yaɗa Labarai na Karamar Hukumar, Abdu Bako Abdullahi (ANIPR), ya ruwaito cewa lamarin ya haddasa asarar dukiyoyi masu daraja, inda ya yi kira ga Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya duba halin da al’umma suka shiga.
Ya ce sake fasalin asibitin zai taimaka wajen farfaɗo da hidimar kiwon lafiya a yankin, musamman ma matakin farko.
Alhaji Abubakar ya kuma yaba wa jami’an tsaro da Hukumar Kashe Gobara kan yadda suka tashi tsaye wajen dakile wutar cikin gaggawa.
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News6 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
