Connect with us

News

One Kano Agenda Ta Shirya Taron Kwanaki Biyu Kan MatsalolinTattalin Arziki Da Siyasar Kano

Published

on

IMG 20251212 WA0000

Kungiyar One Kano Agenda ta bayyana cewa tana shirye-shiryen gudanar da wani babban taro na kwanaki biyu da zai mayar da hankali kan matsalolin tattalin arziki da siyasar Kano, tare da samar da mafita masu dorewa.

A cewar kungiyar, burinta shi ne ganin an samu hadin kai a tsakanin al’ummar Kano, tare da gina tushen shugabanci mai inganci da ci gaba da ya shafi kowa ba tare da wariya ba.

Ibrahim Little Zai Garzaya Kotu Kan Yunkurin Ganduje Na Kafa Hisba Mai Zaman Kanta A Kano

Kungiyar ta ce taron zai mayar da hankali ne kan hanyoyin farfado da tattalin arzikin jihar da kuma inganta halartar jama’a cikin siyasa, musamman matasa da kungiyoyin fararen hula.

Taron zai tattaro masana, ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, kwararru, matasa da shugabannin al’umma domin tattauna matsaloli da hanyoyin da za a bi wajen bunkasa Kano

Rana ta Farko: Tattalin Arziki

A cewar One Kano Agenda, rana ta farko za ta tattauna batutuwa kamar:

Advertisement

Matakan dawo da Kano matsayinta na cibiyar kasuwanci

Inganta masana’antu da kananan masana’antu (SMEs)

Hanyoyin jawo masu zuba jari

Koyon dabarun cigaba daga jihohi kamar Lagos

Kafa taswirar hanyoyin farfado da tattalin arzikin Kano

Kungiyar ta ce an yi tsammanin taron zai samar da sabbin dabaru da za su inganta ayyukan yi da kasuwanci a jihar.

Advertisement

Rana ta Biyu: Siyasa

Rana ta biyu za ta maida hankali kan:

Inganta shiga jama’a cikin harkokin siyasa

Karfafa matasa wajen zama masu ruwa da tsaki a siyasarsu

Rage rikice-rikicen siyasa da manipulashen al’umma

Gina siyasar da ta dogara da ci gaba, ba batun bangaranci ba.

Advertisement

Kungiyar ta ce wannan muhawara za ta taimaka wajen cusa tunanin siyasa mai amfani ga ci gaban jihar.

One Kano Agenda ta ce taron ya zama dole saboda jihar Kano na cikin wani lokaci da ke bukatar tattaunawa ta gaskiya da tsare-tsaren da za su tunkari manyan kalubale.

Kungiyar ta yi kira ga jama’ar Kano, ciki har da matasa, ‘yan kasuwa da shugabannin al’umma, da su mara wa shirin baya tare da bayar da gudummawa wajen tsara makomar jihar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending