News
Kotu Ta Aike Da Tsohon Ministan Kwadago Chris Ngige Gidan Yari
Wata babbar kotun tarayya da ke Gwarimpa, Abuja, ta bayar da umarnin a tsare tsohon ministan ƙwadago, Chris Ngige, a gidan yarin Kuje, bayan gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhuma takwas da suka shafi cin hanci da rashawa.
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da tsohon ministan a gaban mai shari’a Mariam Hassan, inda ake zarginsa da aikata laifuka a lokacin da yake rike da mukamin ministan ƙwadago a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari. EFCC ta bayyana cewa Ngige ya yi amfani da matsayinsa wajen bai wa abokansa kwangiloli ba bisa ƙa’ida a lokacin da yake kula da NSITF daga Satumba 2015 zuwa Mayu 2023.
Ngige ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa a zaman kotun. Mai shari’a Mariam ta dage ci gaban shari’ar zuwa ranar Litinin domin sauraron bukatar neman belinsa, tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a gidan yarin Kuje har sai an kammala sauraron buƙatar.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
