Connect with us

News

Babba Dan Agundi: Karramawar Digirin Girmamawa Ta Nuna Nagartaccen Shugabancin Gwamna Namadi

Published

on

IMG 20251214 WA0010

Darakta Janar na hukumar kula da ingancin ayyuka ta Kasa (National Productivity Centre – NPC), Dakta Baffa Babba Dan Agundi, ya taya Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, murna kan digirin digirgir na girmamawa (Honoris Causa) da Jami’ar Tarayya ta Otuoke da ke Jihar Bayelsa ta ba shi a fannin Kasuwanci da Dorewa wajan kawu gaba.

A cikin wata sanarwa da ya aikewa manema labarai a ranar 14 ga Disamba, 2025, Babba Dan Agundi ya bayyana cewa an ba gwamnan karramawar ne bisa abin da ya kira nagartaccen shugabanci da jajircewa wajen tafiyar da mulki cikin gaskiya.

Shugaban Karamar Hukumar Rimin Gado Ya Kaddamar Da Aikin Gina Katafariyar Gadar Kogin Karofin Yashi

Ya ce Gwamna Namadi ya taka rawa a gyaran harkokin gwamnati, bunƙasa aikin noma, inganta ilimi, ƙarfafa matasa da kuma haɓaka tattalin arzikin Jihar Jigawa.

“Wannan karramawa tana nuna irin gudunmawar da gwamnan ke bayarwa a hidimar jama’a da kuma ƙoƙarin samar da ci gaba mai ɗorewa,” in ji Daraktan-Janar ɗin.

Babba Dan Agundi ya ce karramawar ba ta shafi Gwamna Namadi kaɗai ba, illa har da al’ummar Jihar Jigawa baki ɗaya, inda ya bayyana ta a matsayin abin alfahari ga jihar.

Ya kuma yaba wa Jami’ar Tarayya ta Otuoke bisa yadda ta karrama abin da ya kira nagarta da ƙwarewa a harkokin manufofin jama’a da shugabanci, yana mai cewa hakan na ƙarfafa sauran masu rike da muƙaman gwamnati su rungumi gaskiya da ladabi.

Advertisement

Daraktan-Janar ɗin ya kammala da yi wa Gwamna Namadi fatan ƙarin nasara da basira wajen ciyar da Jihar Jigawa gaba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending