News
Dan Jarida A Kano Aminu Abdullahi Ya Shirya Horarwa Da Raba Audugar Mata Kyauta.
Wani dan jarida a Jihar Kano kuma ma’aikacin Premier Radio, Alhaji Aminu Abdullahi Ibrahim, ya shirya wani taron horaswa tare da rabon audugar mata kyauta domin wayar da kan jama’a kan yadda ake kula da kai yayin jinin al’ada da kuma tallafa wa mata marasa galihu.
Taron, wanda aka gudanar a ranar Lahadi a dakin taro na PR Nigeria, ya mayar da hankali ne kan ilmantar da mata da maza hanyoyin tsafta da kula da lafiya yayin jinin al’ada, tare da raba audugar mata ga mata 20 da suka halarta.
Masu halartar taron sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi lafiyar mata, hanyoyin kare kai daga kamuwa da cututtuka, da kuma yadda al’umma za su tallafa wa mata da audugar mata — musamman wacce ake iya sake amfani da ita.
Da yake jawabi, wanda ya shirya taron, Alhaji Aminu Abdullahi Ibrahim, ya ce makasudin shirya bitar shi ne wayar da kan jama’a tare da nuna wa maza cewa suna da rawar takawa wajen tallafawa mata yayin jinin al’ada.
“Ba mata kadai ke da alhakin wannan batu ba. Maza ma suna da muhimmiyar rawa wajen tallafa musu ta fuskar fahimta, goyon baya da samar da kayan bukata,” in ji shi.
Ya kara da cewa yana da shirin shirya irin wannan taro duk bayan wata uku domin ci gaba da ilmantarwa da kuma tallafawa mata.
Shi ma wani dan jarida, Tukur S. Tukur, ya jaddada muhimmancin sanya audugar mata cikin abubuwan da ake bai wa amarya a matsayin lefe, yana mai cewa hakan na daga cikin bukatun yau da kullum na mata.
A nata bangaren, daya daga cikin masu bayar da horo, Hajiya Amina Sabiu Musa, ta ce lafiyar jinin al’ada ba karamin batu ba ne, domin yana shafar lafiyar al’umma baki daya.
Ta yabawa yadda taron ya hada maza da mata wuri guda, tana mai cewa hakan ya taimaka wajen fahimtar juna da kuma gano hanyoyin magance kalubalen da mata ke fuskanta.
“Iyaye su sani cewa ‘ya’yansu amana ne, don haka ya wajaba su ba su tarbiyya mai kyau tare da ilimantar da su kan wadannan muhimman batutuwa,” in ji ta.
Ita ma Maryam Abbas Muhammad, wacce ta gabatar da bayani kan tsaftar kai yayin al’ada, ta bukaci al’umma da su rika tallafawa mata marasa karfi da audugar mata domin kare su daga kamuwa da cututtuka.
Ta ce mata da dama na bukatar tallafi na ilimi da kayan tsafta, musamman audugar da ake iya sake amfani da ita.
Taron ya samu halartar masana da wakilan kungiyoyi daban-daban na cikin al’umma, inda suka jaddada bukatar ci gaba da wayar da kai kan lafiyar mata a matakin iyali da na al’umma.
