Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Da ASUU Za Su Kaddamar Da Sabuwar Yarjejeniya Domin Inganta Ilimi A Najeriya

Published

on

Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) sun shirya bayyana wata gagarumar yarjejeniya da aka kulla domin karfafa zaman lafiya da inganta karatu a jami’o’in kasar nan jibi Laraba.

Advertisements
Advertisements

Mai magana da yawun ma’aikatar ilimi, Folasade Boriowo, ta ce za a gudanar da taron kaddamar da wannan yarjejeniya ne a babban dakin taro na hukumar TETFund da ke Abuja, karkashin jagorancin Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, da kuma Minista a ma’aikatar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad.

Advertisements

Rikicin Manoma da Makiyaya Ya Yi Ajalin Mutane 10, Ciki Har da Kansila A Taraba 

A cewar Madam Folasade, wannan yarjejeniya wani muhimmin mataki ne na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin inganta yanayin koyarwa da koyo da kuma sanya jami’o’in Najeriya su zama masu gogayya da sauran jami’o’in duniya.

Advertisements
Advertisements

Gwamnati ta jaddada cewa wannan mataki zai kara dawo da kwarin gwiwa ga dalibai da ma’aikata, tare da tabbatar da cewa an samu dorewar sauye-sauyen da za su samar da ingantaccen ilimi mai amfani ga daukacin ‘yan Najeriya

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending