Connect with us

News

Yan Najeriya Na Shan Fiye Da Lita Biliyan 2.5 Na Ruwan Leda A Duk Shekara — Gwamantin Tarraya 

Published

on

pure water

Hukumar Kare Muhalli ta Ƙasa, NESREA, ta ce ’yan Najeriya na shan fiye da lita biliyan 2.5 na ruwan leda (pure water) a duk shekara, wanda sama da masana’antun samar da ruwan leda 32,000 ke samarwa a faɗin ƙasar.

Babban Daraktan NESREA, Farfesa Innocent Barikor, ya bayyana hakan ne a Abuja yayin taron fara aikin GEF Child Project 11193, mai taken “Hanyoyin Zagaye na Rage Gurɓatar Filastik a Najeriya”.

Advertisement

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mutane Huɗu, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi Masu Yawa A Kano 

Barikor ya ce shirin na da nufin rage yawan amfani da ruwan leda , tare da tabbatar da cewa jama’a na samun ruwan sha mai tsafta.

Ya bayyana cewa ruwan leda, duk da sauƙin samunsa ga al’umma, ya zama babbar matsala ga muhalli, inda ya haddasa toshe magudanan ruwa, ambaliya, lalacewar muhallai da kuma barazana ga lafiyar jama’a.

Advertisement

“Kalubalen samun ruwan sha da matsalar gurɓatar filastik suna tafiya tare, shi ya sa wannan aiki ya zama mai muhimmanci,” in ji Barikor.

 

Advertisement

NAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending