News
China Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Kan ‘Yan Yahoo-yahoo 11
Kasar China ta zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane 11 dake da alaka da kungiyoyin ‘yan daba, wadanda suka kware wajen zamba cikin aminci ta hanyar amfani da wayoyin hannu da kuma intanet.
Wannan hukunci ya shafi ‘yan kungiyar laifuka ta Ming, wadanda suka yi suna wajen damfara ta wayoyin hannu da intanet, gudanar da cibiyoyin zamba, hada-hadar miyagun kwayoyi da ayyukan bata gari a Myanmar.
China Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Kan ‘Yan Yahoo-yahoo 11
Daga cikin wadanda aka hukunta akwai Ming Guoping da ‘yar jikinsa Ming Zhenzhen. Sun kasance manyan shugabanni a wasu cibiyoyin zamba masu ma’aikata kusan 10,000.
Wani tsohon dan majalisar kasar, Ming Xuechang, ya kashe kansa a gidan yari kafin hukunci, yayin da sauran ‘yan kungiyar suka gamu da hukuncin bayan iyalansu sun samu damar ganinsu a karo na karshe.
Hukuncin ya biyo bayan shekaru na koke-koke daga iyalan wadanda suke safarar da kuma kulawar kafafen yada labarai na kasa da kasa, kafin hukumomin Beijing su karye cibiyoyin kungiyar a 2023.
Hukumomi sun bayar da umarnin kama ‘yan kungiyar tun a watan Nuwamba, 2025, tare da lada ga duk wanda ya taimaka wajen kamo su, tsakanin $14,000 zuwa $70,000.
-
News4 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
