Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Lalata Sansanin ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane A Kwara

Published

on

An yi wata musayar wuta tsakanin sojojin Najeriya da tawagar dan ta'adda Bello Turji

Jami’an runduna ta 22 tare da hadin gwiwar ofishin mai bai’wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu sun lalata sansanonin ‘yan bindiga da dama tare da kubtar da wadanda aka yi garkuwa da su a ya yin gudanar da ayyuka a fadin jihar Kwara.

Harin wanda aka kai tsakanin ranakun 23 zuwa 29 ga watan Janairun 2026 a karkashin Operation Igbo Danu, inda aka gano wasu yankuna da ƴan ta’adda su ke a Jihar, ciki har da garin Garin Dandi da ke karamar hukumar Ifelodun ta Jihar.

Advertisement

Ragewa Da Kara Farashin Man Fetur Da Matatar Man Dangote Ke Yi Ka Iya Jefa Nigeria cikin Masharsharar Tattalin Arziki —Yan Kasuwa

Babban kwamandan runduna ta biyu ta sojojin Najeriya kuma kwamandan sashe na uku na Operation FANSAN YAMMA Manjo Janar Chinedu Nnebife, ya ce sojojin sun yi nasarar tarwatsa sansanonin ƴan ta’adda da kwato makamai, inda hakan ya sanya ƴan ta’addan su ka tsere daga maboyar ta su.

Advertisement

Acewarsa a musayar wutar da a ka yi ya kai ga hallaka ɗan ta’adda daya, ya yin da wasu kuma su ka tsere dauke da harbin bindiga.

Ya kuma bayyana cewa an kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su a ya in gudanar da ayyukan.

Advertisement

Ya yi kira ga mazauna yankin da su taimaka wa hukumomin tsaro da bayanan da za su taimaka wajen dakile ayyukan ƴan ta’addan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending