Connect with us

News

Kotu Ta Yankewa Tsohon Shugaban NEXIM Hukuncin Daurin Shekaru 490

Published

on

Robert Orya

Wata Kotu dake Abuja ta ɗaure tsohon shugaban Bankin NEXIM, Robert Orya shekaru 490 a gidan yari, saboda samun sa da laifin zambatar Bankin kuɗaɗen da suka kai kusan naira biliyan 2 da rabi.

Mai shari’a F.E. Messiri a Abuja ya gabatar da hukuncin ɗaurin shekaru 10 akan tuhume tuhume 10 da aka yiwa wanda ake zargin, bayan an tabbatar da laifi a kan sa.

Advertisement

An kama yan Najeriya 109 kan zargin safarar kwayoyi a Indiya

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon shugaban bankin inda ta tuhume shi da aikata laifuffuka 49 lokacin da ya rike mukamin sa tsakanin shekarar 2009 zuwa 2016.

Advertisement

Bankin NEXIM na da matukar tasiri a bangaren tattalin arzikin Najeriya, la’akari da yadda gwamnati ta karkata ayyukan sa wajen tallafawa bangaren kasuwancin da bai da nasaba da man fetur.

 

Advertisement

 

VANGUARD

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending