Connect with us

News

Mutum 2 Sun Rasu Sakamakon Faɗawa Rijiya A Kano

Published

on

images (4)

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da rasuwar mutane biyu bayan faɗawa rijiya a yankuna biyu dake jihar .

Advertisements
Advertisements

Mai magana da yawun hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce matashi mai shekaru 18, Yusif Malam Gwani Isah, ya faɗa wata rijiya a Kwanar Madugu, ƙaramar hukumar Ungogo. Hukumar ta aika da ƙungiyar ceto, amma matashin ya rasu kafin a kai shi asibiti.

Advertisements

Mutum 2 Sun Rasu Sakamakon Faɗawa Rijiya A Kano

Advertisements
Advertisements

A wani lamari daban, wani yaro mai shekaru 8, Abdussalam Ibrahim, ya faɗa rijiya a Kofar Yamma, ƙaramar hukumar Karaye. Ƙungiyar ceto ta isa wurin cikin gaggawa, amma yaron ya rasu.

Hukumar ta yi ta’aziyya ga iyalan mamatan sannan ta yi gargadi ga jama’a da su kula da yaran su.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending