Connect with us

News

Duk Da Kashe Sama Da Naira Tiriliyan 7, Matsalar Wutar Lantarki Na Ci Gaba Da Addabar ’Yan Najeriya ‎

Published

on

Wutar Lantarki

‎Duk da kashe makudan kudade da suka haura Naira tiriliyan 7 a bangaren wutar lantarki cikin sama da shekaru goma da suka gabata, ’yan Najeriya na ci gaba da fama da matsalar rashin ingantacciyar wuta.

‎Binciken jaridar Daily Trust ya nuna cewa tun daga shekarar 2013, lokacin da gwamnatin tarayya ta mika aikin samar da wutar lantarki ga kamfanoni masu zaman kansu, an kashe biliyoyin kudade da nufin inganta samar da lantarki a fadin kasar.

Advertisement

Jama’a Sun Hallaka Wani Wanda Ake Zargi Da Ƙwaƙule Idanun Ɗan Maƙwabcinsa A Nasarawa

Sai dai duk da wannan jari mai yawa, Najeriya ba ta kai ga samun wutar lantarki mai dorewa da tabbas ba.

Advertisement

‎A cikin watan farko na shekarar 2026 kadai, manyan biranen kasar sun fuskanci katsewar wuta sau biyu sakamakon faduwar layin wutar lantarki na kasa (national grid), lamarin da ya sake jefa al’umma cikin duhu tare da dagula harkokin kasuwanci da rayuwar yau da kullum.

 

Advertisement

‎Masana da masu sharhi kan harkokin makamashi na bayyana cewa ci gaba da faduwar wutar lantarki na hana bunkasar tattalin arziki tare da rage ingancin rayuwar jama’a, duk da kudaden da aka zuba a bangaren a karkashin gwamnatocin shugabanni hudu da suka gabata.

‎Rahoton ya kara nuna cewa har yanzu ana bukatar gyare-gyare masu zurfi, tsare-tsare masu inganci da kuma gaskiya wajen tafiyar da bangaren wutar lantarki, domin tabbatar da cewa kudaden da ake kashewa na haifar da sakamako mai amfani ga al’ummar Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending