Connect with us

News

INEC Ta Saka Ranar Zaɓen 2027 A Najeriya

Published

on

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar da jadawalin manyan zaɓuɓɓukan kasar na shekarar 2027, inda ta bayyana muhimman ranakun zaɓe da na zaɓen fidda gwani na jam’iyyun siyasa da yakin neman zaɓe, da rajistar masu zaɓe.

Hukumar ta ce za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar tarayya ranar Asabar, 20 ga Fabrairun 2027, yayin da zaɓen gwamna da na majalisun jihohi za su biyo baya bayan makonni biyu, wato ranar 6 ga Maris, 2027.

Advertisement

Yau Shekaru 50 Da Kisan Janar Murtala Ramat Muhammad

Game da yakin neman zaɓe kuma, jam’iyyun siyasa da ‘yan takara za su fara yakin neman zaɓe na shugaban ƙasa da majalisar tarayya daga ranar 18 ga Nuwambar 2026 zuwa 19 ga Fabrairun 2027.

Advertisement

Yakin neman zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi zai fara daga ranar 15 ga Disambar 2026 kuma ya ƙare a ranar 5 ga Maris, 2027, awanni 24 kafin ranar zaɓe kamr yanda BBC ta ruwaito

Hukumar ta sanar da cewa rajistar masu zaɓe zai fara a watan Afrilun 2026, kuma ya ƙare a watan Janairun 2027 domin bai wa ‘yan ƙasa damar yin rajista ko sabunta bayanansu.

Advertisement

Haka kuma, jam’iyyun siyasa za su gudanar da zaɓen fidda gwani tsakanin 1 ga Yuli da 30 ga Satumbar 2026, sannan su miƙa sunayen ‘yan takararsu a ranakun tsakanin 1 da 31 ga Oktobar 2026.

Hukumar ta ƙara da cewa za ta fitar da jerin sunayen ‘yan takara na ƙarshe ranar 15 ga Nuwambar 2026.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending