Connect with us

News

Hadarin Mota Ya Yi Ajalin Mutum 14 A Hanyar Dawowa Daga Daurin Aure

Published

on

Akalla mutane 14 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya auku yayin da wasu baki ke dawowa daga liyafar daurin aure a birnin Umuahia, babban birnin Jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya.

‎Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar, yayin da fasinjojin ke dawowa daga bikin daurin aure da aka gudanar a Enugu. Motar bas kirar coaster da ke dauke da su ta yi karo gaba da gaba da wata babbar motar tirela, lamarin da ya jawo asarar rayuka da dama.

Advertisement

Dakarun Soji Sun Ƙwato Zunzurutun Kuɗi Naira Miliyan 37 Da Za A Kai Wa Ƴan Bindiga A Borno

‎Lamarin ya auku ne a kan titin Enugu–Port Harcourt Expressway, kusa da University of Nigeria Teaching Hospital, a wani wuri da ke dab da mahadar 4-Corner.

Advertisement

‎Shaidun gani da ido sun bayyana cewa hatsarin ya faru da misalin karfe shida na yamma, inda mutane 14 suka mutu nan take, yayin da wasu daga cikin wadanda suka jikkata suka rasu daga baya a asibiti.

‎ Wadanda suka tsira na ci gaba da karbar magani sakamakon munanan raunukan da suka samu.

Advertisement

‎Rahotanni sun nuna cewa yawancin mamatan ‘yan kasuwa ne masu sayar da kayan abinci a yankin Bonny Street da ke kusa da Owerri Road da Isi Gate a Umuahia.

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILY POST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending