Connect with us

News

Iran Ta Tabbatar Da Kisan Ali Khamenei Da Iyalansa

Published

on

fe9dabbb381ab477f8dd4408245e7fb00de97a4634d31b09fb87d8d5f0bdff4a

Kafar watsa labaran gwamnatin Iran ta ce an kashe Jagoran Addinin ƙasar Ayatollah Ali Khamenei a harin da Isra’ila da Amurka suka kai, lamarin da ya sanya kiraye-kiraye ga rundunar juyin-juya-hali ta Revolutionary Guards domin ta ɗauki matakin ramuwar gayya.

Gidan talbijin na ƙasar Iran ranar Lahadi ya sanar da makokin kwana 40 tare da bayar da hutun kwana bakwai bayan kisan shugaban addinin ƙasar mai shekara 86, wanda ke kan mulki tun shekarar 1989.

Advertisement

Jami’an ’Yansanda Sun Dakatar Da Wasan Tashe A Kano

Kafofin watsa labaran Iran sun ruwaito cewa a kashe ‘yar Ayatollah Ali Khamenei da jikarsa da kuma surukinsa a harin.

Advertisement

“Shahadar da shugaban addini ya yi ba za ta sa a manta da tafarkinsa da jagorancinsa ba, hasali ma, za a tabbatar da su ne bisa ƙarfin gwiwa da jajircewa,” a cewar mai gabatar da labarai a gidan talbijin na gwamnatin Iran.

Rundunar juyin-juya-hali ta Revolutionary Guards ta sha alwashin yin ramuwar gayya kan “wadanda suka kashe” Khamenei.

Advertisement

“Rayuwar gayya da ƙasar Iran za ta yi zai kasance mai tsanani kuma cike da karsashi, sannan waɗanda suka kashe Shugaban Al’umma ba za su ci bulus ba,” in ji wata sanarwa da Rundunar juyin-juya-hali ta fitar.

An kashe jagoran addinin Iran lokacin da yake taro da na hannun damansa

Advertisement

Harin da Isra’ila da Amurka suka kai Iran ranar Asabar ya zo ne a lokacin da Khamenei yake gudanar da taro da manyan masu ba shi shawara, a cewar wsu majiyoyi na gwamnatin Amurka.

Isra’ila ta yi iƙirarin cewa an kashe Khamenei ne tare da manyan na hannun damansa da suka haɗa da Ali Shamkhani, tsohon sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa, da Mohammad Pakpour, kwamandan Rundunar juyin-juya-hali ta Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC).

Advertisement

 

TRT AFRIKA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending