Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Dakile Hare-haren Da Mayakan ISWAP Suka Kai Sansanonin Sojoji 5 A Borno 

Published

on

‎Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya Da Take Rike Da Su Na Tsawon Kwanaki 10

Dakarun soji na Operation HADIN KAI sun daƙile hare-haren da mayakan ISWAP suka kai kan sansanonin sojoji guda biyar a lokaci guda a wuraren Delwa da Goniri da Kukawa da Mainok da kuma wani matsugunin sojoji da ke dajin Sambisa na Jihar Borno a daren Lahadi 8 zuwa Litinin 9 ga Maris 2026.

Jaridar PRNIGERIA ta ruwaito cewa wannan na cikin sanarwar da Jami’in Yaɗa Labaran Operation HADIN KAI Laftanar Kanal Sani Uba ya fitar a ranar Litinin 9 ga Maris 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa mayakan ISWAP sun kai hare-haren ne daga bangarori da dama a lokaci guda domin kokarin mamaye sansanonin sojojin.

Sai dai dakarun sojojin sun mayar da martani tare da samun goyon bayan karin dakaru da kuma bangaren jiragen yaki na Operation HADIN KAI wanda ya taimaka wajen dakile hare-haren.

Bayan artabun, sojojin hallaka wasu daga cikin su, sun kuma kwato wasu makamai da kayan yaki da ƴan taʼaddar suka bari yayin da suke arcewa.

Sai dai artabun ya lalata katangar tsaro a Goniri da Kukawa tare da lalata wasu gine-gine da motoci a sansanonin.

Advertisement

Sanarwar ta ce duk da hare-haren, sojojin Operation HADIN KAI na ci gaba da rike dukkan wuraren da aka kai harin, yayin da ake gudanar da karin bincike da sintiri a yankunan domin kamo mayakan da suka jikkata da suka tsere zuwa garuruwa makwabta.

Sai dai rundunar ta ce wasu sojoji sun rasu a yayin artabun.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending